Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow tare da Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow yana Abuja inda yake ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wata ziyara ta musamman da yake yi a Najeriya.

Shugabanni sun tattauna a kebe ba tare da barin ‘yan jarida sun shiga wajen tattaunawar ba.

Mista Barrow ya iso fadar Shugaban kasa da misalin karfe 11:50 na safiyar ranar talata, kuma wannan shi ne karon farko da Shugaban kasar ta Gambiya yake ziyara a Najeriya tun bayan zaman Shugaban kasar Gambiya a watan Janairun 2017.

An kuma ci abincin rana tsakanin Shugabannin biyu a fadar Shugaban kasa dake Aso Villa.

Dan shekaaru 51, Adama Barrow shi ne mutumin da ya kawo karshen mulkin shekaru 21 na Yahya Jameh wanda yanzu haka yake kasar Ikwaturiyal Gini yana gudun hijira.

Shugaba Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da mika mulki daga Jameh zuwa Barrow a lokacin da aka shiga hautsinin siyasa a kasar.

Kungiyar raya tattalin kasan Afurka na yamma ECOWAS su ne suka nada Buhari a matsayin mutumin da zai shiga tsakani a kasar ta Gambiya domin daidaita al’amura a kasar.

NAN

LEAVE A REPLY