Shugaba Buhari

 

Hassan Y.A. Malik

Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Mambilla da ke fama da yawan rikice-rikice kafin ya bar Nijeriya zuwa Ghana don halarstar cikar kasar Ghana shekaru 61 da samun ‘yancin kai a yau Litinin 5 ga wata.

Haka kuma shugaba Muhammadu Buhari zai tarbi shugaban kasar Liberia, shugaba George Weah a Abuja kafin ya rankaya zuwa jihar Taraba.

Tuni dai mukarraban shugaba Buhari suka sauka a Taraba don kammala shirye-shiryen tarbarsa.

Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa Buhari zai gana da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki na jihar don ya dada jan hankulansu kan hanyoyin da za a bi don kawar da tashe-tashen hankula da rikicin kabilanci ke haddasawa.

Rikicin kabilanci na baya-baya nan dai ya yi sanadiyyar akalla rayukan mutane 20 inda shanu akalla 300 suka salwanta ko dai ta hanyar kashe su ko kuma sace su.

Yankin Mambilla na shan fama da rikice-rikicen addini a baya-bayan nan. Rikicin ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama tare asarar dukiya mai yawa.

Shugaba Buhari zai mika zuwa Accra ta Ghana da zarar ya kammala abinda ya kai shi Taraba.

LEAVE A REPLY