Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da katafaren kamfanin giya mafi girma a yankin yammacin Afurka a jihar Osun.

Kamfanin Breweries International PLC shi ne zai gina wannan katafaren kamfani a rukunin masana’antu na Flowergate dake titin Sagamu-Abeokuta a jihar Ogun ranar Talatar makon gobe.

Kamfanin IB wani reshe ne na AB InBev group kamfanin da yake samar da giya mafi girma a duniya.

Wannan kamfanin giya da Shugaba Buhari zai kaddamar a makon gobe shi ne irinsa na hudu a Najeriya bayan wanda yake Ilesha da Anaca da kuma Fatakwal.

Ana sa ran kashe dalar Amurka miliyan 250 domin gina wannan katafaren kamfanin giya.

LEAVE A REPLY