Shugaba Muhammadu Buhari

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar gida Nijeriya a gobe Litinin don gabatar da wata ziyarar aiki a birnin London.

Shugaba Buhari zai yi wata tattaunawa kan dangantaka tsakanin kasar Birtaniya da Nijeriya da Firaministar Birtaniya, Therasa May gabanin taron kasashe rainon Ingila da za a yi tasakanin 18 zuwa 20 ga Afrilun, 2018

Haka kuma Shugaba Buhari zai gana da shugaban kamfanin Royal Dutch Plc, Mista Ben van Buerden, kan batun sanya hannun jari a harkokin man fetur din Nijeriya ta hanyar kamfanin mai na Shell da adadin jarin zai kai dalar Amurka biliyan 15.

Har ila yau, Buhari zai gana da zai gana da babban limamin cocin Ingila na darikar Angalika, Archbishop na Canterbury, Rabaren Justin Welby, wanda amini ne ga Shugaba Buhari, musamman kan batun alakar addinai a Nijeriya.

Daga karshe kuma, Shugaba Buhari zai gana da wasu muhimman ‘yan Nijeriya mazauna Birtaniya

LEAVE A REPLY