Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba yayi sabbin nade nade guda biyu,inda ya nada Jafaru Momoh a matsayin babban daraktan asibitin kasa dake Abuja da kuma Nwadinigwe Uwatoronye a matsayin babbandaraktan asibitin kashi na kasa dake Enugu.

Babban daraktan yada labarai na ma’aikatar lafiya ta kasa Boade Akinola shi ne ya bayyana sanarwar nada mukaman ga ‘yan jaridu.

Akinola ta ce wadannan sabbin nade nade zasu fara aiki ne daga ranar 5 ga watan Yulina shekaraanan 2018.

A cewarta, tuni Ministanlafiya na kasa Isaac Adewole ya taya mutanan biyu murnan samun wannan sabon mukami da suka yi.

Ministan kuma ya bukac da suyi aiki tsakani da Allah da kokarin ciyar da harkar lafiyar kasarnan gaba.

NAN

LEAVE A REPLY