Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sufeton ‘an sanda na kasa, Ibrahim K. Idris ya kai kansa fadar Shugaban kasa yayi bayanin yadda akai ake muzgunawa ‘yan hamayya musamman a birnin tarayya Abuja.

Wata majiya mai tsuhe ta shaidawwa Daily Nigerian cewar, Sufeton ‘yan sanda ya bi umarni inda ya shiga fadar shugaban kasa da safe, inda aka bukace shi yaje ya dawo zuwa anjima.

“SHugaban kasa da mataimainsa da kuma Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa suna ta wata tattaunawa bayan tattaunawa a fadar Gwamnati, inda aka bukaci Sufeton ‘yan sanda na kasa da ya jira a dakin da ake jira don ganin Shugaban kasa”

“A halin da ake ciki, mataimakin Shugaban kasa da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa na kattaba wata wasikar dake dauke da bayanan sauke Sufeton ‘yan sanda na kasa”

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbaji da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole sune kan gaba wajen kiran da a sauke Sufeton ‘yan sanda na kasa daga mukaminsa.

 

LEAVE A REPLY