Shugaba Muhammadu Buhari
Daga Hassan AbdulMalik

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya kori kodinatan shirin afuwar gwamnati ga tsagerun Neja delta (Coordinator Amnesty Programme), Birgediya Janar Paul Boroh, inda nan take ya maye gurbinsa da Farfesa Charles Dokubo.

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan yau Talata a Abuja.

Farfesa Dokubo, kafin nada shi sabon mukaminsa shi ne daraktan bincike da nazari a cibiyar  al’amuran da suka shafi kasa-da-kasa ta Nijeriya da a turance a ke kira da Institute of International Affairs.

Farfesan ya yi digirinsa na uku akan nazarin kimiyyar daburan tafikar da aikin gwamnati a jami’ar Bradford ta Amurka.

Farfesa Dokubo dan asalin garin Abomena ne, da ke karamar hukumar Akuku-Toru ta jihar Ribas.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ya fara wani bincike kan yadda shirin na afuwar gwamnati ya gudanar da ayyukansa tun daga shekarar 2015 kawo yanzu.

A cewa Mista Femi Adesina, za a karkata binciken ne kan yadda al’amuran kudade suka shiga suka fita a shirin,da kuma wasu abubuwa da suka zama cikas ga aiwatar da shirin yadda gwamnati ta shirya.

LEAVE A REPLY