Edward Adamu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Edward Adamu a matsayin mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, tuni dai Shugaban ya aike da sunan Adamu zuwa zauren majalisar dattawa domin tantancewa.

Mai taimakawa Shugaban kasa kan al’amuran yada labarai Femi Adeshina ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

A cewar sanarwar, Adamu wanda ya fito daga jihar Gombe,zai maye gurbin Sulaiman Barau wanda dan asalin Zariya ne daga jihar Kaduna, wanda yayi ritaya a Disambar 2017.

Shi dai Adamu ya shafe kusan shekaru 25 yana aiki a babban bankin kasa na CBN, an kuma nada shi a matsayin Daraktan tsare tsare a shekarar 2012.

Daga nan ya samu cigaba zuwa Daraktan gudanarwa a shekarar 2016 inda daga wannan mukamin ake son mayar da shi mataimakin Gwamnan Babban bankin.

NAN

LEAVE A REPLY