Aliyu Gusau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon Ministan tsaro Janar Aliyu Mohammed Gusau mai ritaya bisa rasuwar mai dakinsa Hajiya Binta.

A wata wasikar ta’azaiyar da Shugaban ya aikewa iyalan Aliyu Gusau, ya mika t’aziyarsa a madadin al’ummar Najeriya bisa ga wannan babban rashi da suka yi.

Shugaban yayi adduah da fatan Allah ya jikan Hajiya Binta ya gafarta mata, sannan ya bukaci iyalan da su dauki hakuri da dangana na wannan rashi da suka yi.

LEAVE A REPLY