Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin tura karin jami’an tsaro zuwa jihar Zamfara domin fuskantan kalubalen tsaron da jihar  take fama da shi a ‘yan kwanakin nan na kashe kashen mutane babu gaira babu dalili.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da tawagar kungiyar Malaman Musulmi karkashin majalisar koli ta tabbatar da Shariaha Najeriya ta kai masa ziyara a fadar Gwamnatin tarayya dake Aso Villa a Abuja babban birnin tarayya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, jihar Zamfarata jima tana fama da ayyukan ta’addanci da suka hada da satar mutane da yin garkuwa da su a cikin daji da satar shanu da kuma kaiwa garuruwa farmaki inda ake kone garin kuma a kashe mutanen garin.

Shugaba BUhari ya shaidawa majalisar koli tatabbatar da Shariah a Najeriya cewar, yana yin dukkan mai yuwuwa wajen ganin an kawo karshen abinda yake faruwa a jihar Zamfara na tashe tashen hankula da kashe kashen rashin Imani iyakacin iyawarsa.

 

LEAVE A REPLY