Shugaban kasar Afurka-ta-Kudu Cyrill Ramaphosa

Shugaban kasar Afurka-ta-Kudu Cyrill Ramaphosa a ranarLaraba ya bayyana cewar tuni Gwamnatinsa ta dauki kwakkwaran mataki kan ‘yan kasar da suke kashe baki ‘yan wasu kasashen Afurka.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi yayi babban taron Bankin harkar ciniki da masana’antu na yankin Afurka dake gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Ramaphosa ya bayyana cewarrashin aikin yi na daga cikin babban dalilin da ya sanya ‘yan kasarsa suke kashe baki ‘yan wasu kasashen a kasarsa.

Shugaban ya tabbatar da cewar zasu sanya kafarwando daya da duk wanda aka kama da laifin kashe bakin ‘yan kasashen waje. “Da sannu zamu share wayen duk wadan da aka ci zarafinsu dan su ba ‘yan Afurka-ta-Kudu bane”

LEAVE A REPLY