Qaloon Muazu

Kasancewa Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) kwararre ne a bangaren siyasa saboda horo da marigayi Shehu Musa Yar’adua ya bashi da kuma dadewa da yayi yana harkar, ya sanya magautansa suke kai gwauro su kai mari wajen neman wani abu mai muni da zasu jefe shi dashi.

Hakan ne ya sa ake yi masa sharri da cewa ya tsani talaka. Sai kaji an ce yace Allah baya karbar addu’ar talaka, ko kaji ance yace talakawa kamar kaji ne idan aka jefe su da hatsi zasu bika da sauran sharrace-sharrace da basu da madafa. Sai ka tambayi hujja sai a tsaya ana zare idanu. Hakazalika, zaka ji magautan Wazirin Adamawa suna cewa wai shi barawo ne. Wannan ba komai bane ya jawo haka sai tsole wa magautansa ido da Wazirin Adamawa yayi.

Babu wanda zaka ji yace Atiku ba kwararre bane wajen aiki, sai dai kaji sun ce maka wai barawo ne. Abunda zai nuna maka cewa labarin kangen kurege ne shine:

1. Tun 2002 Obasanjo ya tsani Atiku saboda ya so ya kalubalance shi a zaben wannan 2003. Amma tun daga wannan lokacin Obasanjo da yayi kaurin suna wajen sauke shugabannin majalisar dattijai da na tarayya bai samu damar saukeshi ya hada shi da hukumar EFCC ba, haka sukayi shekara hudu baya sonshi amma babu yadda ya iya dashi.

2. A 2007, Obasanjo ya samu damar daura yaronsa Marigayi Umaru Musa ‘Yaradua, amma duk da haka basu samu damar kama Atiku da laifin sata ba a shekara uku da yayi akan mulki.

3. Goodluck Jonathan ya hau mulki a 2010, yayi shekara biyar akan mulki amma bai samu damar kama Atiku da laifin sata ba duk da kalubalantarsa da yayi tayi a zaben fidda gwani na 2011 da komawarsa APC a 2014.

5. Shugaba Buhari da muka zabeshi a 2015 da alkawarin zai yaki cin hanci da rashawa ya shafe shekara uku da kusan rabi akan mulki amma har yanzu bai samu nasarar kama Atiku da laifin sata ba.

6. Alhaji Atiku Abubakar ya fito ya kalubalanci duk wanda yake zarginsa da sata da ya fito da hujjoji ya nuna haka, har yanzu shiru kake ji kamar Malam yaci shirwa.

A lokacin da Yahudawa da Nasara sukayi ikirarin cewa babu mai shiga aljannah sai wanda ya kasance Bayahude ko Banasare, sai Allah yace wa Annabin tsira (SAW) yace musu su kawo hujjojinsu in sun kasance masu gaskiya.

LEAVE A REPLY