Sheikh Yakubu Musa Katsina

An yi kira ga ‘yan Majalisar tarayya da suka hada da Majalisar Dattawa da kuma ta tarayya da su yi kokarin su yi abinda ya kamata sannan su bar shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya yi aikin da zai amfani talakawa ko kuma su hadu da talakawa a zabe mai zuwa.

Shiekh Yakubu Musa (sautus-sunnah) dayadaga cikin jiga-jigar kungiyar Izala, ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa damanema labarai a Katsina.

Sheikh Yakubu Musa ya kuma kara da cewa lokacin ya yida yakamata a ce ‘yan majalisa sun yi karatun ta nutsu wajan baiwa shugaban kasa damar yin abinda ya kamata domin amfanin talakan Najeriya.

Shehin Malamin ya ce talakawa suna sane da duk abinda ke faruwa a majalisun nan guda biyu saboda abubuwan da suka bayyana yanzu shi ne, ‘yan majalisar suna yin abinda zai kare mutuncin su ne kawai ba wai wadanda suka tura su domin su wakilce su a majalisar ba.

Ya ce kin sakawar ‘yan majalisa marar da shugaban Muahammadu Buhari ya yi ba zai ba su damar kin abinda bai kamata ba, wannan a cewarsa anan cutar da talakawa da kuma rusa kasa baki daya anakuma azabtar da talaka, wanda ya ce wajibi ne a matsayinsu na shuwagabanni su tabbatar an yi abinda zai amfani talakawa ba wai abinda zai kare mutuncin aljihunsu ba.

Sheihk Yakubu Musa ya ce talakan Najeriya ya yarda cewa Buhari Ba barawo bane, kuma ya yi imanin cewa Buhari yana son taimakawa Nijeriya ne, ba ya zi bane domin sace kucdin Najeriya ba ya kai wani wurin ba, ko da ya samu matsala a siyasa to ayi masa ajizanci na dan adam.

Daga nan sai ya yi kira ga sanatoci tunda daga shugaban majalisar har zuwa na kasada cewa su aje yi makamansu su zauna, susami shugaban kasa su tattauna da shi, akan abinda zai amfanin Nijeriya.

Ya kuma yi kira ga tsofafin shuwagabanni da suke zaune a gefe guda suna bada umarnin ana kulle-kelle ga gwamnatin Buhari ya zama wajibi acewarsa da su ji tsoron Allah, Allan da ya kawo Buhari akanmulki yana nan, gwamnatin baya tana da sojoji tana da kudi tana da komi amma Allah ya ba Buhari mulki to wallahi su ji tsoron Allah.

Ya yi masu tambihi da cewa ya zama wajibigare su da su bada hadin kai domin yin abinda zai taimaki kasa da kuma ‘yan kasa, sannan su taimaka wajan ganin an dawo da kudadan da wasu kiraye suka sace a gwamnatin baya domin fitar da Nijeriya daga halin da take cikin a wannan yanayi.

Katsinaposthausa.com

LEAVE A REPLY