Ustaz Tijjani Bala Kalarawi, Wani Malamin addini a jihar Kano

Sanannen Malamin addinin nan na jihar Kano, Tijjani Bala Kalarawi yadauki gabarar sulhunta tsakanin tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Dangantaka ta tabarbare tsakanin tsohon Gwamnan wanda Sanata ne a yanzu mai wakiltar Kano ta tsakiya a zauren majalisar dattijai ta Najeriya, da kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki ya ja daga da tsohon mai gidan nasa.

A lokacin da yake zantawa da ‘yan jaridu a birnin Kano, Tijjani Bala Kalarawi ya bayyana cewar rikici tsakanin gaggan ‘yan siyasar biyu zai janyowa jihar mugun koma baya.

A cewarsa, wannan satoka-sa-katse da ake yi tsakanin mutanan biyu, ba komai bane sai aikin Shedan wanda yake tunzura mutanan biyu basa ga miciji da juna.

Malamin yace, ba zai yuwuw a zuba ido ana ganin manyan ‘yan siyasar biyu suna wannan batarnaka ba, yace zai sulhunta su ko dai a Makkah ko kuma a Madina a kasar Saudiyya.

“Wannan rikici tsakanin masoya kuma Shugabannin ba dace ba o kadan. Yana da illah da kuma lahani ga cigaban jihar Kano. Ina da yakinin cewar wannan sabani aikin Shedan ne”

“Muna bukatar muyi adduah ta musamman akan wannan rikici. Akwai abin takaici ace mutanen irin wadannan suna da irin wannan mugun sabani da juna”

“Da yardar Allah, Ni zan shiga tsakaninsu, domin samar da maslaha kan wannan rikici. Zan gana da su amma ba a najeriya ba, a Makkah ko a Madina” A cewar Kalarawi.

Haka kuma, Tijjani Bala ya bukaci al’umma da su taya shi da adduah kan Allah ya bashi nasarar wannan aiki da ya sa a gaba.

LEAVE A REPLY