Sanata Shehu Sani

Sanata Sulaiman Hunkuyi dake jagorantar ‘yan adawar cikin gida na jam’iyyar APC a jihar Kaduna ya bayyana cewar zasu fice daga jam’iyyar ta APC zuwa wata jam’iyyar ‘yan watanni kafin babban zaben kasa na 2019 dake tafe.

Kungiyar ‘yan adawar da aka fi sani da sunan APC Akida, sun fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a inda suke bayyana cewar sun gama dukkan wasu shirye shirye na tsallakewa su bar jam’iyyar da suka himmatu wajen ginawa tare da kashe mata makudan kudade wajen gnin ta kai bantenta a jihar Kaduna.

Fitattaun mutane a cikin wannan hadaka da zasu balle daga cikin jam’iyyar ta APC sun hada da Sanata Shehu Sani da tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kaduna Isa Ashiru Kudan da Tom Maiyashi da sauransu.

LEAVE A REPLY