Daga Hassan Y.A. Malik

Masu binciken lafiya sun gargadi mata da su guji shan maganin Paracetamol ko da kadan ne a lokacin da suke dauke da juna biyu.

A wani sakamakon bincike da aka wallafa a kundin bincike mai suna ‘Reproduction’, an bayyana cewa paracetamol ka iya rage mazantakar jarirai maza da matantakar jarirai mata, kuma wannan zai taba rayuwarsu har lokacin da suka girma.

Haka kuma binciken ya bayyana cewa maganin zai iya rage wa yara mata da maza yiwuwar iya haihuwa a lokacin da suka girma.

Binciken wanda aka gudanar akan beraye maza ya gano cewa maganin ya rage samuwar sinadarin da ke sanya mazantaka wato ‘Testosterone’ a jikin berayin a lokacin da suke a ciki.

A yayin da suka girma, berayin sun kasa nuna halaye irin na maza kamar yadda sauran berayen ke nunawa ba.

Daya daga cikin wadanda suka gudanar da binciken, Farfesa David Mabjerg Kristensen na Jami’ar Copenhagen a kasar Denmark, ya ce abunda binciken ya nuna shi ne, Paracetamol na hana samuwar sinadarin Testosterone, kuma raguwa a sinadarin Testosterone ya na hana berayen su zama cikakkun maza.

A cewar shi “Akwai damuwa a tattare da wannan lamari”

LEAVE A REPLY