Budurwar da saurayinta ya kashe ta

Rundunar ‘yan sandar jihar Ondo a Najeriya ta ce an gano gawar ‘yar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo Khadijat Oluboyo a gidan wani mutum Adeyemi Alao da ‘yan sanda su ka ce saurayinta ne.

An gano gawar ne bayan shafe kwanki iyayen Khadijat, wato iyalan tsohon mataimakin gwamnan jihar Lasisi Oluboyo sun sanar da ‘yan sanda cewa ta bace.

Kakakin rundunar Femi Joseph ya bayyana wa BBC cewa, saurayin nata da wasu abokansa sun yi mata wani abu, sai saurayin nata ya haka rami a gidansa ya binne ta.

“Amma bayan kwana uku zuwa hudu sai gawar ta fara wari, hakan yasa dole ya kira kaninsa ya ce ya je ya samo masa buhu wanda zai sa gawar ya kaita wani wuri. To ana cikin haka ne muka samu labari muka je muka kama shi,” in ji Femi.

Ita dai yarinyar daliba ce da ke shekarar karshe a jami’a kuma ta shaida wa iyayenta cewa za ta yi tafiya ne, amma sai ba su kara ji daga gare ta ba, hakan ya sa suka sanar da ‘yan sanda.

Sai dai rundunar ba ta yi karin haske ba akan ko me ake zargin Adeyemi da abokan nasa sun yiwa marigayiyar ba.

Tuni dai rundunar ta kame saurayin nata da ake zargi kuma tana ci gaba da bincike.

Ko a kwanan baya ma rundunar ta ce an daure wata mata wadda aka samu da laifin kashe saurayinta.

A cewar kakakin ‘yan sandan jihar, wannan dai ba shi ne karo na farko da irin haka ya taba faruwa ba, don a baya-bayan nan an daure wata mata wadda aka samu da laifin kashe saurayinta.

BBCHAUSA.COM

LEAVE A REPLY