Hassan Y.A. Malik

A wani lamari mai matukar daure kai, wani saurayi mai suna Chiadi Ezeibekwe, dan shekaru 25, ya auri kanwarsa ta ciki daya, mai shekaru 17, bayan da ya bi dare ya dirka mata ciki.

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Agba da ke karamar hukumar Ekwulobia, cikin jihar Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa dan uwan saurayin mai suna Chijioke ne ya daura auren a wani coci da ke garin, inda ya bada hujjar cewa addininsu ya halarta irin wannan aure.

Sai dai jama’a mabiya cocin da dama ba su gamsu da wannan batu ba, lamarin da ya hasala matasan garin, suka kuma yi yunkurin kone cocin bayan da labarin afkuwar abinda suka kira shaidanci ya game kauyen.

Yayin da ta ke magana da manema labarai, Mahaifiyar ango kuma mahaifiyar amarya, ta ce babu wani laifi a abinda ‘ya’yanta suka aikata, tunda dai Chiadi ya biya ‘yar uwarsa sadaki.

Rahotanni sun bayyana, tuni dai Sarkin kauyen ya bukaci iyalin gaba daya su bayyana a gabansa domin su amsa tambayoyi.

LEAVE A REPLY