A halin da ake ciki ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda 24 sun sanya hannu a takardar tsige kakakin majalisar Yusuf Ata, abinda yake nuna sauran mutum uku kacal keyar kakakin majalisar ta taba kasa.

Binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewar, a da an samu mutum21 da suka sanya hannu a takardar tsige kakakin majalisar, inda babu jimawa adadinsu ya karu zuwa 24, abin ya nuna sauran mutum 3 kacal ake jira su sanya hannu a takardar domin tsige kakakin majalisar.

Tuni dai ‘yan majalisar suka tsige mai tsawatarwa na majalisar Labaran Madari, dan majalisa mai wakiltar Warawa a majalisar dokokin, yayin shima mataimakin SHugaban masu rinjaye Butu-Butu ya taba kasa a yau Talata.

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kanon da aka tsige kwanakin baya, Alhassan Rurum shi ne yake jagorantar ‘yan majalisar 24 wajen ganin an tsige Yusuf Ata daga zaman kakakin majalisar dokokin jihar ta Kano.

 

LEAVE A REPLY