Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Saad III

Daga Hassan AbdulMalik

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a yau Juma’a, ya yi kira ga Musulmi a fadin Nijeriya da su fita duban jaririn watan Rajab na shekarar 1439 bayan hijira.

Kiran na Mai alfarma Sarkin Musulmin ya fito a wata sanarwa da ke dauke da sa hannun wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Junaidu, wanda shi ne shugaban kwamitin shura kan harkokin addinin Musulunci na fadar Sarkin Musulmi.

“Muna sanar da al’ummar Musulmi cewa, gobe Asabar, 17 ga watan Maris, 2018 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Jimada Thani, 1439 ne ranar da za a sanya idanu kan tabbatar da tsayuwar watan Rajab, 1439.

“A saboda haka muna kira ga Musulmi da su sanya idanu wajen duban watan a gobe Asabar, kuma su taimaka wajen sanar da masu unguwanninsu, dagatansu ko hakimansu don labarin ya isa ga Sarkin Musulmi,” kamar yadda sanarwar ta ce.

Sarkin Musulmi, a sanarwar tasa ya bukaci Musulmi da su ci gaba da yi wa kasa addu’a don samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kai tsakanin ‘yan kasa ta yadda kasar za ta kai ga samun ci gba mai dorewa.

LEAVE A REPLY