Sarkin Musulmi Sultan Saad Abubakar III

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Saad Abubakar III ya ja hankalin Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da sauran ‘yan siyasar jihar Kaduna da su dena jifan juna da miyagun kalamai, duba da cewar zaben 2019 na kara kusantowa.

Idan za’a iya tunawa a ranar29 ga watan Maris, Sanatocin jihar Kaduna, sun takawa kudurin Gwamna El-Rufai na ciwo bashin bankin duniya birki, ta hanyar kin amincewar da Majalisar dattawa ta yi ga Gwamnatin jihar  da ta ciwo bashin.

Haka kuma, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a lakcar gab da Ramadan da kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta shirya a Kaduna, Sarkin Musulmi ya kalubalanci salon maganganun Gwamnan Kaduna na yin kalamai marasa dadi ga ‘yan siyasar jihar, inda yake tsine musu.

Sarkin Musulmin yayi kira ga ‘yan siyasar jihar Kaduna da su rungumi yadda zasu zauna da juna lafiya, domin samun dorewar zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY