Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III ya baiwa kungiyar Miyatti-Allah watanni biyu, da su bankado masu hannu wajen kashe kashen fulani a Najeriya.

Sultan Sa’ad Abubakar, wanda shi ne Shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya NSCIA, ya bayar da umarnin ne a lokacin da ake bikin rantsar da sababbin zababbun kungiyar ta Miyatti-Allah a Sakkwato ranar Talata.

Haka kuma, Sarin Musulmin ya bukaci sabbin zababbun Shugabannin kungiyar da su binciko masa, ko Fulani suna da hannu a kashe kashe da ake jingina musu ka a’a a fadin tarayyar Najeriya, a cewarsa ana kashe Fulani da yawa, amma kafafen yada labarai basa basu muhimmancin da ya dace.

“Haka kuma, muna baku wa’adin watanni biyu, da ku kewaya Najeriya baki daya ku gano mana, me yasa ake zargin Fulani da kashe kashe a kasarnan”

“Kuje ku gano mana, shin Fulanin da ake zargi da yin kashe kashen nan da gaske su din ne. Sannan ku binciko mana ko wasu ne suke yinwadannan kashe kashe da sunan Fulani ake jingina abin ga Fulani, muna bukatar jin gaskiyar wannan lamuran da suke faruwa daga gare ku”

“Bama jin takaicin a kiramu da sunan Fulani a ko ina  ne, saboda Fulani ba fitinannun mutane bane. Domin yanzu dukkan wani abu na ta’addanci da kashe kashe sai a jingina shi ga Fulania Najeriya”

“Muna da masaniyar ako wadanne irin jama’a akwai mutanan kirki da kuma gurbatattu, haka nan tsakanin Fulani ma ba za’a rasa irinsu ba. Ba daidai bane ace duk wani aikin ta’annati sai ace Fulani ne suka yi”

LEAVE A REPLY