Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar III

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Na uku ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a yau Alhamis, inda ya bayyana cewargobe Juma’a daya ga watan Shawwal inda take ranar Sallah. Hakan kuma yana nuna karewa kwanakin watan Ramadan mai alfarma da aka azumta.

Sarkin ya bayyana cewar anga watan a garuruwa kamar haka, Kano da Zariya da Barno da Kaduna da kuma Jos, sultan ya ayyana ranar Juma’a gobe a matsayin ranar Sallah a dukkan fadin Najeriya.

Sannan yayi kira ga al’umma da su gudanar da shaglgulan bukukuwan Sallah lami lafiya ba tare da tashin hankali ko nuna kyama ga juna ba.

Daily Nigerian Hausa na taya dumbin al’ummar Musukmi Barka da Sallah.

LEAVE A REPLY