Marigayi Sarkin Katagum, Muhammadu Kabir Umar

An bayar da sanarwar rasuwar Mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Muhammadu Kabir Umar. Sarkin ya rasu ranar Asabar da yamma a garin Azare dake yankin masarautar Katagum a ranar 9 ga watan Disamba.

Sarkin dai ya taba rike mukamin ministan ilimi a zamanin Gwamnatin marigayi firimiyan jihar Arewa Sa Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto.

Allah ya jikansa ya gafarta masa.

LEAVE A REPLY