Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose

Hassan Y.A. Malik

Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II tare da shugaan kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa gabaki daya, Alhaji Muhammadu Kiruwa, sun yabawa, tare kuma da nuna goyon bayansu da dokar kiwo wasa-rai-rai da gwamantin jihar Ekiti bisa jagoranci gwamna Ayodele Fayose ta kafa.

Shugabannin biyu sun bayyana cewa dokar za ta tsare ‘yanci da mutuncin bangarori biyun da abin ya shafa baya ga wanzar da zaman lafiya da fahimta da dokar za ta haifar da makiyaya da monoma.

Haka kuma, gwamnatin jihar Ekiti ta dau alkawari yafewa duk makiyayin da ya mika makamansa ga jami’an tsaron jihar.

An gabatar da wannan tattaunawa ce a yau Litinin a fadar gwamnatin jihar Ekiti, inda Sarkin Kano ya samu wakilcin tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau.

Sarkin Kano ya koka kan yadda wasu bata gari ke fakewa da rigar fulani makiyaya suna aikata munanan laifuka wanda hakan ke kara haifar da rashin yarda da fulani makiyaya daga sauran al’umma.

LEAVE A REPLY