Shugaban majalisar dattawa kuma mai neman takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Bukola Saraki ya ziyarci tsohon Gwamnan Jigawa kuma mai neman takarar Shugaban kasa Sule Lamido a mahaifarsa dake Bamaina.

Saraki yaje jihar Jigawa je domin ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP tare da neman goyon bayansu akan aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Sule Lamido da Bukola Saraki dukkan su na neman jam’iyyar PDP ta amince musu yi mata takarar Shugaban kasa a zaben 2019 dake tafe.

LEAVE A REPLY