Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Wani sanatan PDP Enyinnaya Abaribe wanda yake wakiltar jihar Abiya ta gabas a majalisar dattawan Najeriya, ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar shi ‘turun jahili ne’ da bai san komai ba.

Mista Abaribe wanda yake tofa albarkacin bakinsa kan wani kuduri da aka gabatar gaban majalisar kan kashe kashen da aka yi a jihar Kogi wanda ake zargin makiyaya da aikatawa, inda yace Shugaban na da dabi’ar komai bai sani ba.

Wannan caccaka da aka yiwa Shugaba Buhari, Sanata Ataai Aidoko Ali shi ne ya kalubalanci kisan daaka yiwa mutane 32 a kananan hukumomin jihar Kogi guda biyu a ranar larabar da ta gabata.

Mista Abaribe ya ce “Na gamsu da batun Shugaban masu rinjaye na majalisa inda yace dole mu yi aiki tukuru domin aiki tare da bangaren majalisar zartarwa”

“Abun da kawai ban yarda da shi ba sh ne, wadan nan bangaren zartarwa da kuke son ko da yaushe mu yi aiki tare da su, basu cika yarda da abinda yake na wajibi akansu ba”

“Muna da Shugaban kasar da zai ce, ban sani ba, ban san ina Sifeton ‘yan sanda na yake ba, Shugaban kasar da ko da yaushe yake cewar ban san ya aka yi haka ta faru ba. Ko abubuwa na kusa kusa sai yace bai sani ba”

 

LEAVE A REPLY