Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, tsohon Gwamnan jihar Sakkwato kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Sakkwato ta Arewa ya dauki nauyin dalibai 51 domin yin karatun digirin farko a jami’ar Al-Hekma dake jihar Kwara.

Sanatan ya bayyana cewar zai cigaba da daukar nauyin dalibai suna yin karatu a fannoni daban daban domin ragewa iyayensa da kuma Gwamnati dawaniya. Sanata Wamakko wanda yayiwa daliban gargadin su zama wakilai na gari a inda zasu yi karatu.

Sannan ya bukace su da su yi kokari wajen sun baiwa marar da kunya tare da maida hankali wajen abinda suka je yi a jihar ta Kwara. Da yake mayar da martani, daya daga cikin daliban da suka ci gajiyar wannan tallafin Karatu na Sanata Aliyu Wamakko Bin Sunusi Sakkwato ya yi godiya ga Sanata Wamakko kan wannan dawainiya da yayi musu.

 

LEAVE A REPLY