Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, yayi tur da matakin da Gwamnatin el-Rufai ta ɗauka na korar ma’aikatan kananan hukumomi a faɗin jihar. Sanatan yayi wannan kamai ne a shafinsa na facebook a ranar talata. Inda ya bayyana abin da cewar rashin Imani ne da rashin tausayi na Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufai.

“Wannan korar da suka yi wa ma’aikata ba komai ba ne, banda zalinci da mugunta da cin zarafi da wannan Gwamnan ya saba nunawa mutanen jihar Kaduna, tun daga lokacin da ya hau kan karagar mulkin jihar”

“Jihar Kaduna na samun isassun kuɗaɗe daga kason wata wata na asusun gwamnatin tarayya, domin biyan albashi, saboda haka babu wani dalili na korar ma’aikata da Gwamnati take yi”

“Gwamnan Kaduna yana gallazawa mutane ne, sabida yana ganin yafi karfin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sannan kuma, yana ganin yafi karfin Shugabancin jam’iyyar APC, amma abinda bai sani ba, shi ne, bai fi karfin Allah ba”

Sannan kuma, sanata yayi kakkausar suka akan yadda aka zura ido Gwamna el-Rufai na cin mutunci da zarafin wanda yaga dama. Ya kuma tunasar da Gwamnan cewar, ya sani, shima akwai lokaci na zuwa da al’ummar jihar Kaduna zasu nuna mishi iyakarsa.

“Duk wanda yaci mutuncin mutane, da duk wanda ya goyi bayan cin mutuncin mutane azzalimi ne, bai cancanci a sake koyon bayansa ba, dan haka, kada jama’a su sake zaben wannan mutumin”

“Ya koreku a yau, lokaci yana zuwa da kuma zaku koreshi; ya rushe ku a yau, lokaci yana zuwa da kuma zaku rushe shi; ya kakkabeku a yau,lokaci yana zuwa da kuma zaku kakkabe shi,In sha Allah”

Bayan haka kuma, Sanatan ya ci alwashin cewar, zasu yi dukkan abinda zasu iya wajen ganin an mayar da duk wanda aka kora daga aiki ya koma bakin aikinsa, tun daga kan hakimai da malaman makaranta da su kansu ma’aikatan kananan hukumomi.

“Malaman makarantu da aka kora da hakimai da aka kora da kuma ma’aikatan kananan hukumomi da aka kora, ku yi hakuri zaku koma bakin aikinku, nan ba da jimawa ba, bayan wannan Gwamnatin da mukarrabanta sun kau”

A farkon wannan makon ne dai gwamna ya sa aka fara sallamar ma’aikatan kananan hukumomi daga ayyukansu, inda akai ta yayata abin a kafafen sada zumunta na intanet da aka fi sani da ‘Socialmedia’.

LEAVE A REPLY