Sanata Shehu Sani

Matasan jam’iyyar PDP mai hamayya na matsawa Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani lamba akan ya sallama jam’iyyarsa ta APC ya dawo jam’iyyar PDP, domin a cewar matasan Shehu Sani yafi dacewa da jam’iyyar tasu.

Wata kungiyar matasan PDP ta kasa ta yi taron manema labarai karkashin Shugabanta na kasa Inipribo Tamunotonye da kuma sakatariyar kungiyar inda suke kira ga Sanatan da ya sallama jam’iyyarsa ta APC ya dawo PDP.

A cewar matasan bai kamata Sanatan ya cigaba da zama cikin jam’iyyar ba alhali ana wulakanta shi da kuma cuguna masa, suna sanar da shi cewar, PDP nan ne inda yafi dacewa da shi da irin gwagwarmayar da yake yi da azzalumai.

LEAVE A REPLY