Sanata Barnabas Gemade

Sanata Barnabas Gemade ya caccaki Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari akan kokarin share al’ummar Tibi da ake yi daga doron kasa.

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Yakubu Danjuma ya kalubalanci sojojin Najeriya da sakaci wajen barin ana kashe al’umma a jihar Taraba, abinda ya sanya tsohon ministan kira ga al’ummar jihar da su tashi domin baiwa kawukansu da dukiyoyinsu kariya.

Da yake magana,a gaban babban zauren majalisar dattawa a ranar Talata, Sanata Gemade yace “Abinda yake faruwa a Najeriya, ya nuna wasu mutane sunfi karfin hukuma. Domin kuwa, muna ganin yada ake kokarin share wasu al’umma daga doron kasa”

“Abin takaici ne da kaico, ace Gwamnati ta zuba ido tana kallon ‘yan ta’adda suna cin karensu babu babbaka a yau”

“A maimakon Gwamnati ta tashi tsaye domin daukar matakan da suka dace, sai kawai aka auka batun ba mu da laifi ko ba mu bane, ana kallon anki daukar matakan da suka dace domin yin abinda ya dace”

“Abinda ya faru a kudancin jihar Nasarawa, yana faruwa ne akan kabila ta kadai, wanda suna da yawan gaske a jihar Nasarawa ta kudu. Irin wannan kashe kashe shi ne dai ake yi a kananan hukumomin Goma da Logo da Gwer ta yamma duk a jihar Binuwai”

“Haka kuma, shi ne dai abinda muke gani a Wukari da karamar hukumar Takum a jihar Taraba. Kawai ana son gamawa da tsirarun kabilu ne, wanda muka fito daga cikinsu”

“an san dalilin da zai sanya mutane akilai da za’a zabe su domin kare rayuwar mutane, amma daga baya sai su juya musu baya”

“Ace, har yanzu akwai mutanen da suke dauke da makamai suna kashe wanda suka ga dama, dan sun san ba abinda zai faru. Ana haka, yayin da sifeton ‘yan sanda na kasa yake yawo a jirgin helkwafta abinsa, ya sauka a Kasuwa wai yana tambayar mutane ko suna da abarin batagari”

“Ana yin duk wannan tsiyataku, babu wani matakin kawo karshen na hakika da ake dauka. Wannan abin takaici ne”.

LEAVE A REPLY