Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin jihar Jigawa ta shelanta cewa mutane 14 ne cutar Sankarau ta yi sanadiyyar mutuwarsu, a yayin da akalla mutane 51 ke fama da cutar a kananan hukumomin jihar 10.

Kwamishinan lafiyar jihar, Dakta Abba Zakari, ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya Laraba a Dutse, fadar gwamnatin jihar.

Dakta Zakari ya ci gaba da cewa, mutum guda ya rasu a karamar hukumar Birnin Kudu, a Gagarawa kuwa an samu mutum guda da ya kamu da cutar amma babu mutuwa, haka kuma a Jahun akwai rahoton mutum bakwai, nan ma babu mutuwa.

A Malam Madori kuwa, mutane 10 aka samu da Sankarau kuma a ciki mutane 4 sun mutu. A Ringim, mutum guda aka samu, amma babu mutuwa, haka a Miga. A Babura an samu mutane 11 da cutar Sankarau, amma babu ko mutum guda da ya mutu. A Dutse ma an samu mutum guda da cutar, amma a nan din ma babu rahoton mutuwa izuwa yanzu.

Karamar hukumar Maigatari ta samu mutum 3 da Sankarau, amma babu mutuwa. A Taura an samu mutum 10, kuma 5 sun mutu.

Dakta Zakari, ya ci caga da cewa, a cikin mutane 51 da ke killace bisa zargin Sankarau tun daga watan Nuwanbar 2017 zuwa yanzu, mutum 10 ne aka tabbatar da cewar Sankarau ce ke damunsu, ragowar 41 din zargi ne dai ake yi.

LEAVE A REPLY