Wasu ‘yan Najeriya su uku an samu gawarwakinsu yashe cikin wani daki a yankin Uttam Nagar dake Mohan Garden a babban birnin Delhi a ranar Juma’a.

Rundunar ‘yan sandan kasar Indiya sun garzaya wajen tare da kaddamar da binciken musabbabin mtuwar mutanan uku.

Babu wani tabbataccen bayani da ya nuna dalilin mutuwarsu, haka kuma, babu alamun an ji musu rauni ko yi musu duka a jikinsu.

 

LEAVE A REPLY