An sau barkewar cutar kwalara ayankin Gashuwa dake jihar Yobe, ya zuwa yanzu cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 13 a cikin 160 da aka bayar da rahoton sun kamu da cutar a kwanaki shida da suka gabata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na najeriya NAN, ya ruwaito.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewar, babban asibitin kwararru na Gashuwa da aka kai galibin wadanda suka kamu da cutar an samu mutuwar mutum biyar a karon farko a lokaci guda.

Majiyar ta cigaba da cewar galibin waan da suka kamu da cutar sun fito ne daga kauykan Sabon Gari da Katuzu da Zango da Lawan Musa da Sarkin Hausawa, nanne inda aka bayar da labarin inda cutar ta bulla.

Tuni dai Gwamnatin jihar ta tura dakarun ko ta kwana domin ganin cutar bata watsu zuwa wasu sassan jiharda basu kamu da ita ba.

Kwamishinan ruwa na jihar Malam Muhammad Bukar ya tabbatar da tura wata tawaga da zata datse yaduwar cutar, tare kuma da sanya magani a dukkan matattarar ruwa dake yankin da kuma yiwa garin feshin magani.

 

LEAVE A REPLY