Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban hukumar inganta harkar lafiya a jihar Bauchi, Adamu Gamawa, ya tabbatar da barkewar cutar amai da gudawa a jihar.

Ya ce mutane 20 ne izuwa yanzu suka kamu da cutar, a ciki 2 sun rasa rayukan su.

Gamawa ya fadi haka ne a yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce tuni sun dauki matakai kwarara da za su tabbatar cutar ba ta ci gaba da yaduwa ba.

A jiya Talata kuma, Gamawa ya sanar da mutuwar mutane 3 a sakamakon kamuwa da suka yi da cutar zazzabin Lassa a jahar.

Ya ce an samu kimanin mutane 25 dauke da cutar a kananan hukumomi 7 na jahar, wanda suka hada da Alkaleri da Bauchi da Bogoro da Dass da Tafawa Balewa da Toro da Warji.

Ya ce an samu mutane 25 din ne a tsakanin 1 ga watan Janairu da 4 ga watan Maris na shekarar nan.

LEAVE A REPLY