Jonathan Silas Zwingina

Tsohon mataimakin Shugaban masu rinjaye a majalisardattawa ta kasa Jonathan Zwingina ya bayyana cewar samarda ‘yan sandan jihohi a Najeriya shi ne maganin matsalar tsaron da ake fama da ita a kasarnan.

Sanata Zwingina yana wannan bayani ne a lokacin da ya kai ziyara fadar uban kasar Ganye Alhaji Umar Sanda dake jihar Adamawa.

A cewarsa, kirkiro da ‘yan sandan na jihohi zai taimaka matuka wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita a kasarnan, ya kara da cewar hakan kuma ba zai ci karo da aikin rundunar ‘yan sanda na kasa ba.

Zwingina ya cigaba da cewar su wadannan ‘yan sandan na jihohi zasu kasance mataimaka ne ga ‘yan sandan Gwamnatin tarayya domin samun nasarar yin aikinsu cikin sauki tare da cimma burin abinda aka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY