Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar sam shi bai kaiwa tsohon Gwamnan jihar Filato ziyara a gidan kurkuku ba, ya bayyana cewar tun ranarda aka fara Azumi har ya zuwa ranar Litinin dinnan yana Yola jihar Adamawa.

Ofishin tsohon mataimakin Shugaban kasar dake Abuja shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yana nesanta Alhaji Atiku Abubakar  da batun kaiwa Jonah Jang ziyara a gidan yari.

“Mun samu labarin cewar wai tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya kaiwa Jonah Jang ziyara, sam wannan ba gaskiya bane, wasu ne kawai ke son batawa Atiku suna suka kitsa labarin da sunansa”

 

LEAVE A REPLY