Ya zuwa yanzu an yi jana’izar mutane 71 a kauyen Gwaska dake yankin karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, tun bayan wani hari da wasu mahara suka kai kauyen suka kashe mutane da dama.

Wani basaraken gargajiya a yankin ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP cewar an yi jana’izar mutanan da suka rasa rayukansu su 71 yayin da mahara suka far musu a kauyen na Gwaska a Birnin-Gwari.

“Har ya zuwa yanzu ana cigaba da binciken gawarwakin mutane a kauyen” a cewar Sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II.

“Muna fatan matakan da aka dauka na tsaro a yankin su haaifar da da mai ido, na dakile sake aukuwar irin wannan kashe kashe a yankin Birnin-Gwari”

A wata sanarwa da Sakataren Majalisar dinkin duniya, António Guterres yayi Allah wadai da kai wannan hari, inda yayi kira da a binciko wadan da suka yi wannan aikin ta’addanci a gurfanar da su gaban kuliya.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai da ya ziyarci kauyen Gwaska a ranar Litinin, yayi tir da maharan inda yace makiya al’umma ne kuma makiya zaman lafiyar jihar Kaduna.

Tuni dai Gwamnati ta bayar da kafa wata bataliyar soja a yankin Birnin-Gwari da kuma samar da wata Bataliyar ‘yan sanda domin baiwa wajen kariya daga hare haren ‘yan ta’adda, a cewarKakakin Gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

LEAVE A REPLY