Wani rukuni na 'yan matan Chibok

Rundunar sojan Najeriya ta Lafiya Dole da aka tura garin Fulka a ranar Alhamis ta kubutar da wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da Boko Haram suka sace tun cikin shekarar 2014.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar Lafiya Dole, Onyema Nwachuku, ya fitar, binciken farko farko ya bayyana cewar daya daga cikin matan da aka kubutar mai suna Salomi Pagu na daya daga cikin wadan da aka buga sunayensu a matsayin matan Chibok da ake nema.

“Yanzu wannan yarinya da aka gano wadda ke tare da wata yarinya mai suna Jamila Adams ‘yar shekara 14 tare da jaririnta, suna karkashin kulawar jami’an tsaron rundunar Lafiya Dole suna samun kolawa ta musamman” A cewar Mista Nwachikwu.

LEAVE A REPLY