Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi

Daga Hassan Abdulmalik

Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Farfesa Benard Odoh ya ajiye aikinsa da yammacin jiya Litinin.

Farfesa Odoh ya bayyana dalilin ajiye aikin nasa a matsayin rashin bada dama da gwamnatin gwamna Umahi ke yi ga ‘yan majalisar zartawar jihar na su tofa albarkacin bakinsu a muhimman kudirorin da ke da alaka da ci gaba jihar.

A takardar ajiye aikin da Farfesa Odoh ya yi, ya bayyana cewa daga cikin dalilin da ya sanya ya ajiye aikin shi ne don ci gaba da aikin nasa iya kawo matsala ga dangantakarsa da gwamna Umahi, wanda shi kuma yana martaba dangantakar da ke tsakaninsu.

 Daga karshe, Farfesa Odoh ya yi godiya ga gwamna David Umahi bisa karamcin da ta yi masa na zabo shi don ya yi wa jiharsa aiki a matsayin sakataren gwamnatin jihar

LEAVE A REPLY