Wakilin Muryar Amurka,Nasiru Birnin-Yero

Matar wakilin Muryar Amurka, Nasiru Birnin-Yero da aka yi garkuwa da ita tare da danta, ya bayyana cewar sai da ya biya Naira miliyan biyu ga mutanan da suka yi garkuwa da su, sannan aka sake su.

Masu garkuwa da mutanen, sun kuma kashe ma’aikacin hukumar kula da hanyoyi ta kasa FRSC,mkafin daga bisani su yi garkuwa da iyalan na wakilin Muryar Amurka.

Nasiru Birnin-Yero ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a ranar Asabar a Kaduna cewar, wadan da suka yi garkuwa da iyalin nasa, sun sake su a ranar Juma’a a kauyen Sabon Birni dake daura da filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna.

“A lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kama iyalina, sun nemi na basu Naira miliyan 12 a matsayin kudin fansa domin a sake su”

“Mutanan sun shaida min cewar, sun zo ne domin su yi garkuwa da ni, sai suka yi rashin sa’a basu same ni ba. Suka ce,idan ina son ganin iyalina dole ne na biya kudi ko kuma ni da su har abada”

“Daga nan muka shiga ciniki da masu garkuwa da su, har muka cimma matsaya akan Naira miliyan biyu,wanda sai da muka biya sannan aka sake su”

“Yan uwa da abokai suka yi karo karo aka hada kudin da aka fanso iyalin nawa”

Ya kuma bayyana cewar, iyalin nasa basu samu wata musgunawa ba daga hannun masu garkuwa da su a lokacin da aka tafi da su.

NAN

LEAVE A REPLY