Tsohon GWamnan Naija, Muazu Babangida Aliyu (Talban Minna)

Daga Hassan Y.A. Malik

Tsohon Gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu ya bayyana cewa bai wawushe dukiyar al’umma ba a shekaru 8 da ya yi yana mulkin jihar Neja.

Tsohon Gwamnan ya bayyana haka a yayin da ya ke mayar da martani ga gwamnatin tarayya bisa lika sunansa da ta yi a jerin sunayen wadanda ta fitar a matsayin wadanda gwamnati ta samu dumu-dumu da yi wa dukiyar kasa zagon kasa.

Babangida Aliyu ya bayyana kamfanin dillancin labarai cewa zai kalubalancin sanya sunasa a jerin barayin gwamnati da gwamnatin tarayya ta yi har zuwa tushe.

“Na yi matukar mamakin ganin sunana a jerin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar ta hannun ministan yada labarai, Lai Mohammed, tunda ni babu wanda ya tuntube ni da wata takarda da ta nuna cewa na amfana da Naira biliyan 1.6 daga kudaden makamai da ake zargin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki da handamewa.”

Babangida Aliyu ya ci gaba da cewa, “Ina kalubalantar gwamnati da ta fitar da hujja cewa na amshi kudade daga Sambo Dasuki.”

Ya kuma zargi gwamnatin APC da kokarin yi masa zagon kasa ta hanyar bata masa suna da taba mutuncinsa kawai don ya ki ya shiga jam’iyyar tasu.

LEAVE A REPLY