Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan

Mukaddashin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranar Litinin yayi wata ganawar sirri tare da Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Ahmed Lawan a fadar Shugaban kasa dake Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan ganawa ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ta dulmiya cikin rikici, inda wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawa suka bukaci da Shugaban majalisar Bukola Saraki da yayi murabus daga mukaminsa sakamakon komawarsa jam’iyyar PDP.

Wannan tattaunawana zuwa ne a daidai lokacin da fadar Shugaban kasa ke neman Majalisar dattawan ta dakatar da hutun da ta tafi ta koma bakin aiki domin duba bukatun kasafin kudin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC da kuma sauran batutuwan da suke bukatar tattaunawa.

Sanata Ahmed Lawan yana tare da mai baiwa Shugaban kasa shawara ta fuskar majalisar  dattawa Sanata Ita Enang a yayin wannan tattaunawa da yake yi tare da mukaddashin Shugaban kasa.

LEAVE A REPLY