Marigayi Tijjani Ado Ahmad

Daga Mustapha Usman

Dangin marigayi Tijjani Ado Ahmad wanda ya rasu a ƙasar Amurka yayin da ya je wata ziyarar aiki sun sa ranar da za’a yiwa mamacin janaiza.

Tijjani, wanda sanannen ɗan jarida ne a gidan rediyon Freedom, ya rasu a daren Asabar a birnin Atlanta na ƙasar Amurka.

Ƙanin mamacin mai suna Muhammad ya shaidawa DAILY NIGERIAN HAUSA cewa ofishin jakadancin ƙasar Amurka a Najeriya shi zai dauki nauyin kawo gawar.

Wannan ofishi dai shi ya gayyaci Tijjani ziyarar don kewayawa da zantawa da ɗaliban ƙasarnan da ke karatu a can.

Muhammad ya shaidawa wannan jarida cewa ofishin jakadancin ya bawa ‘yan uwan marigayin biza kuma ya ɗauki nauyin ɗawainiyarsu don su je su taho da gawar.

“Muna sa ran za’a kawo gawarsa ranar Lahadi ko Litinin. Kuma akwai yiwuwar za’a yi janaizarsa a fadar Mai Martaba Sarkin Kano,” inji dan uwan mamacin.

Kafin rasuwarsa, marigayi Tijjani Ado Ahmad shi ke gabatar da shirin Turanci na ‘Greetings from America’ kuma yana daya daga cikin masu gabatar da shirin Barka da Hantsi a Gidan Rediyon Freedom.

Tijjani ya rasu yana da shekaru 39.

LEAVE A REPLY