Tsohon ministan Ilimi MalamIbrahim Shekarau

Tsohon ministan Ilimin Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewar sau da yawa idan kaga an samu sabani tsakanin majalisun dokoki na kasa da bangaren zartarwa to zaka samu laifin Shugaban kasa ne.

Malam Ibrahim Shekarau yana bayanin hakan a wajen wani taro da cibiyar wayar da kai da koyar da zaman aure da kasuwanci a Muslunci ta shiya a dakin taro na kwalejin Shariah ta Malam Aminu Kano dake Kano.

Taron wanda aka yi masa taken “Kasafin kudi a mahangar addini Musulunci” tsohon Kwamishin kasafin kudi na jihar Kano MalamNura Sani Hanga ne ya zama babban bako mai jawabi a wajen taron.

A jawabin nasa, Malam Nura Hanga, ya bayyana cewar, addinin Musulunci bai bar komai kara zube ba, sai da yayi bayanin yadda Musulmi ya kamata yayi mu’amala da shi, ya kara da cewar “Koyarwar addinin Musulunci a cike take da adalci da nuna musulmi yadda zai yi rayuwa musamman harkar kasuwanci”

A lokacin da yake jawabi a matsayinsa na babban bako na musamman a wajen taron, tsohon Gwamnan Kano, tsohon Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewar a sau da dama Shugaba shi ke daukar kaso mafi yawa na sabanin da ake samu tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokokin kan batun kasafin kudi.

“Idan da ace Shugaban kasa yana zama da Shugabannin majalisa su tattauna kan batun kasafin kudi yayi musu bayani su gamsu, suma su maida jawabai, da duk ba’a samu sabanin da ake samu na cushe ko kakaba wani abu a cikin kasafin kudin wanda bangaren zartarwa basu san da shi ba”

“Shi yasa, sau da dama idan kaji ana batun an kakabawa bangaren zartarwa wani abu ko an zabtare wasu kudade a cikin kunshin kasafin kudin kasa, to ba shakka laifin Shugaban kasa ne, domin da shugaban yasa aikinsa, da kafin ya gabatar da kasafin kudin a gaban zauren majalisa ya kamata ya tattauna da Shugabannin majalisar kan batun kasafin”

“Su yi sabani su gama su kadai ba tare da al’ummar kasa sun fahimci akwai wata baraka ko rashin jituwa tsakanin bangaren zartarwa da bangaren majalisa ba kan batun kasafin kudi” A cewar tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau.

LEAVE A REPLY