Hassan Y.A. Malik

Dakarun soja na musamman na ‘Operation Safe Haven’ (OPSH), a jiya Laraba sun yi holin mutune 17 da ke da hannu a kisan kiyashi da ya maimaitu a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato a makon da ya gabata.

Harin na farko dai ya faru ne a daren Asabar, kuma ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutum 100 tare da kone gidaje sama da 50 a kauyuka 11 da karamar hukumar Barikin Ladin.

Kauyukan da aka kaiwa farmakin sun hada da kauyen: Exland, Gashish, Ruku, Nghar, Kura da Kakuruk duk a yankin Gashiish.

Sauran kauyukan sun hada da: Rakok, Kok da Razat su kuma a yankin gundumar Ropp

Dama dai tuni rundunar ta OPSH ta shaidawa mataimakin shugaban kasa Osinbajo a lokacin da ya kai ziyarar nuna alhani da gani da ido cewa sun fara kama wasu wadanda ke da hannu a hare-haren.

A yayin da rundunar OPSH ta yi holin mutanen da ake zargin su 17 a jiya Laraba a shedikwatar rundunar ta musamman da ke a Jos, kakakin rundunar, Manjo Adam Umar, ya shaida cewa, “Wadannan mutane da ku ke gani sune wadanda muka kama zuwa yanzu da muke zargi da hannu a harin ranar Asabar 23 ga watan Yuni, 2018.”

“Munkasa su zuwa aji biyu: 3 daga cikin mutanen, wato Yahuza, Friday da Ahmad na da alaka ne da hari na farko na daren Asabar, inda ragowar 14 kuma ke da alaka da wadanda suka fita wai da nufin daukar fansa, inda suka datse hanyyoyin mota tare da haifar da ta’annati mai yawa.”

“A kokarinmu na dakatar da harin na farko ne muka kama wadannan mutum ukun. Da suka ga jami’anmu sai suka ranta a na kare suka zubar da bindigunsu suka yi cikin daji, inda jami’anmu suka farmu suka yi barazanar harbinsu in basu mika wuya ba.”

Su kuma wadannan sune suka addabi mutane a rabar Lahadi 24 ga watan Yuni, 2018 wai da nufin ramuwar gayya a yankunan Maraba Jama’a, Angludi da Bukuru inda suka haifar da kashe-kashe da asarar dukiya da kuma tayar da hankulan al’umma.”

Da aka tambaye shi ko wadanda aka kama da laifin harin daren Asabar ko ‘yan Nijeriya ko kuma baki ne, sai ya kada baki ya ce, ” ‘Yan Nijeriya ne ba baki ba,” inji Manjo Umar.

Manjo Umar ya ci gaba da bayyana cewa har zuwa yanzu ba su kai ga tsananta bincike ba game da wadanda suka kama din kuma bindigunsu ma irin kirar Hausa ce ba wadanda ake shigo da su daga waje ba.

Manjo Umar ya yi kira ga manema labarai da su fara tuntubarsu game da abinda ya faru ko yake faruwa don samun sahihin labarai a maimakon yada labarin kanzon kurege wanda ba shi da tushe bare makama.

LEAVE A REPLY