A wani hari na baya bayan nan da rundunar sojan saman najeriya ta kai a dajin Kaduna da Zamfara a yau, rundunar a wani taken yaki da ta kira da “Dirar Mikiya” ta yi ruwan bamabamai sansanin ‘yan ta’adda dake dajin Sububu da Rugu dake yankunan jihohin Kaduna da Zamfara.

Wannan bayani na zuwa ne a wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar, Ibikunle Daramola ya fitar, yace sun kai wannan hari ne bayan da suka gano mboyar’yan ta’addar dake yankin Sububu a cikin dajin.

 

LEAVE A REPLY