Rundunar sojan sama ta Najeriya ta tura karin jami’an domin gano ‘yan matan Dapchi da aka sace a makon da ya gabata. Rundunar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta Olatokunbo Adesanya.

Sanarwar tace, Shugaban rundunar sojan sama ta Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar, ya bayar da umarnin tura karin jami’an tsaro domin gano tare da kubutar da wadannan ‘yan mata.

Haka kuma, rundunar ta bayar da wasu lambobin wayoyi da jama’a zasu taimaka da bayanan da zasu kai ga gano tare da kubutar da wadannan ‘yan mata a duk inda suke. Lambobin da za’a kira sune +2348122557720; +2348035733438; +2348172843484; +2348058419128.

LEAVE A REPLY