Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya jinjinawa rundunar sojan Najeriya akan shirinta na samar da Asibitin sojoji a jihar Sakkwato, domin zama babbar cibiyar binciken kwayoyin cututtuka.

Wannan bayani na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar Sakkwato, Imam Imam ya fitar, inda yake cewa, wannan asibitin shi ne irinsa na farko a Najeriya da rundunar sojan zasu kaddamar.

Gwamna Tambuwal ya cigaba da cewa, Asibitin zai kasance wata muhimmiyar cibiyar bincike wadda ta dace da bukatun majalisar dinkin duniya da manyan dakunan gwaje gwajen kwayoyin cututtuka da maganinsu.

Yace, tuni har Gwamnatin jihar ta samarwa da rundunar sojan da wajen da zata yi wannan katafaren Asibiti, inda yanzu aka baiwa rundunar Asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake jihar domin soma gwaji kafin a kammala ginin mazaunin assibitin na din-din-din.

Gwamnan Tambuwal yace, da yawan jihohi sun nemi a samar da wannan katafaren Asibitin a yankunansu, Amma cikin ikon Allah aka zabi jihar Sakkwato domin samar da wannan katafaren asibiti.

“Da farko, ina farincikin sanar da al’ummar jihar Sakkwato cewar, kokarinmu da kwazonmu na bayyanar da irin yunkurinmu na tallafawa duk wani abu da zai kawowa jihar Sakkwato cigaba, shi ne ya janyo mana samun wannan abin alheri”

“Wannan Asibiti da za’a samar, yana da matukar muhimmanci ga rundunar sojan Najeriya, da kuma al’ummarmu gaba daya”

“Akwai cututtuka wadan da suke bukatar zurfafa bincike akansu, sabida irin dumbin al’ummar da ka iya kamuwa da su, don haka dole a gudanar da binciken kwararru kan irin wadannan cututtuka da a irin wannan asibiti ne kadai ake yinsu”

Sannan kuma, Gwamnan ya karyata jita jitar da ake yadawa ccewar, Gwamnatinsa ta hannantawa Sojoji Asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake jihar, inda yayi karin bayanin cewar, an baiwa sojin asibitin ne na dan wani lokaci.

“Mun aikawa majalisar dokokin jihar, wasikar cewar, zamu baiwa sojoji wannan asibiti don su yi amfani da shi na dan lokaci kadan, amma yanayin asibitin yana nan ba zai canza daga yadda mutane suka sanshi ba”

“Sojojin zasu yi amfani da kayyakin dake asibitin, har zuwa lokacin da za’a kammala ginin sabon asibitin Sojojin da za’a samar” A cewar Gwamnan jihar Sakkwato.

 

LEAVE A REPLY