Rundunar sojan kasa ta Najeriya a ranar Litinin ta karyata rahotannin da aka bayar na bacewar wasu sojojin Najeriya da wasu tankokin yaki yayin da suka yi wata kafsawa da ‘yan kungiyar Boko Haram.

Daraktan Rundunar sojan mai lura da sashin hulda da ‘yan jarida Texas Chukwu shi ne ya bayyana hakan a birnin Maiduguri.

Daraktan wanda yake rike da mukamin Birgediya janar, ya yi watsi da wannan rahoton bacewar sojojin tare da cewar batun shaci fadi ne kawai wanda babu kanshin gaskiya a cikinsa.

Ya kara da cewar “Rundunar sojan kasa ta Najeriya tana mai sanar da da al’umma cewar su yi watsi da wancan rahoto na bacewar sojoji, yace kafafen yada labarai ne da basa ganin kokarin rundunar sojin suke yi mata jafa’i”

 

LEAVE A REPLY